1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa!Ku yabi ƙarfinsa a sama!
2 Ku yabe shi saboda manyan abubuwaWaɗanda ya aikata!Ku yabi mafificin girmansa!
3 Ku yabe shi da kakaki!Ku yabe shi da garayu da molaye!
4 Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa!Ku yabe shi da garayu da sarewa!
5 Ku yabe shi da kuge!Ku yabe shi da kuge masu amo!
6 Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!