1 Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa,Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.
2 Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a,Ku daina goyon bayan mugaye!
3 Ku kāre hakkin talakawa da na marayu,Ku yi adalci ga matalauta,Da waɗanda ba su da mataimaki.
4 Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,Ku cece su daga ikon mugaye!
5 “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!Kuna zaune cikin duhu,Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6 Na faɗa muku, ku alloli ne,Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7 Amma za ku mutu kamar kowane mutum,Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8 Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya,Dukan al'ummai naka ne.