Zab 38 HAU

Addu'ar Mai Shan Wuya

1 Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji!Kada ka hukunta ni da fushinka!

2 Ka hukunta ni, ka kuwa yi mini rauni,Ka kuma buge ni har ƙasa.

3 Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani,Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.

4 Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina,Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.

5 Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,

6 An tanƙware ni, an ragargaza ni,Ina ta kuka dukan yini.

7 Ina fama da zazzaɓi,Ina rashin lafiya ƙwarai.

8 An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina,Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.

9 Ka san bukatata, ya Ubangiji,Kana jin dukan nishe-nishena.

10 Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre,Idanuna sun dushe.

11 Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna,Har iyalina ma sun guje mini.

12 Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna,Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni,Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

13 Kamar kurma nake, ba na iya ji,Kamar kuma bebe, ba na iya magana.

14 Ni kamar mutumin da ba ya iya amsawa nake, don ba na ji.

15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji,Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.

16 Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata.Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!

17 Ina gab da fāɗuwa,Ina cikin azaba kullum.

18 Na hurta zunubaina,Sun cika ni da taraddadi.

19 Magabtana lafiyayyu ne masu ƙarfi.Waɗanda yake ƙina ba dalili, suna da yawa.

20 Masu rama nagarta da mugunta,Suna gāba da ni,Domin ina ƙoƙarin aikata abin da yake daidai.

21 Kada ka yashe ni, ya Ubangiji,Kada ka rabu da ni, ya Allahna!

22 Sai ka taimake ni yanzu, ya Ubangiji, Mai Cetona!