1 Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka?Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?
2 Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu,Yana kuwa aikata abin da yake daidai,Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,
3 Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu.Ba ya zargin abokansa,Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.
4 Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su,Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya,Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,
5 Yana ba da rance ba ruwa,Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi.Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.