1 Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!Ku bayin Ubangiji,Ku yabi sunansa!
2 Za a yabi sunansa yanzu da har abada!
3 Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!
4 Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma,Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.
5 Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu.Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,
6 Amma ya duba ƙasa,Ya dubi sammai da duniya.
7 Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.
8 Yakan sa su zama abokan sarakuna,Sarakunan jama'arsa.
9 Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta,Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!