1 Duk wanda ya je wurin MaɗaukakiZai zauna lafiya,Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,
2 Ya iya ce wa Ubangiji,“Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni!Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”
3 Hakika zai kiyaye kaDaga dukan hatsarorin da ka ɓoye,Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu.Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
5 Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,
6 Ko annobar da take aukowa da dare,Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
7 Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,Amma kai, ba za a cuce ka ba.
8 Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.
9 Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,Maɗaukaki ne yake tsaronka,
10 To, ba bala'in da zai same ka,Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.
11 Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai,Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.
12 Za su ɗauke ka a hannuwansu,Don kada ka buga ƙafarka a dutse.
13 Za ka tattake zakoki da macizai,Za ka tattake zakoki masu zafin raiDa macizai masu dafi.
14 Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,Zan kiyaye waɗanda suka san ni.
15 Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala,Zan cece su in girmama su.
16 Zan ba su tsawon rai lada,Hakika kuwa zan cece su.”