1 Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji,Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!
2 Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka,Za ka yi farin ciki ka arzuta.
3 Matarka za ta zama kamar kurangar inabiMai 'ya'ya a gidanka,'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitunSuna kewaye da teburinka.
4 Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya,Hakika za a sa masa albarka kamar haka.
5 Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona!Ya sa ka ga Urushalima ta arzutaDukan kwanakinka!
6 Ya kuma sa ka ka ga jikokinka!Salama ta kasance ga Isra'ila!