Zab 45 HAU

Waƙar Ɗaurin Auren Sarki

1 Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi,Lokacin da nake tsara waƙar sarki,Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.

2 Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,Kai mai kyakkyawan lafazi ne,Kullum Allah yakan sa maka albarka!

3 Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,Kai mai iko ne, Maɗaukaki!

4 Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,Domin ka tsare gaskiya da adalci.Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.

5 Kibanka suna da tsini,Suna huda zuciyar abokan gābanka,Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.

6 Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!Kana mulkin mallakarka da adalci.

7 Kana ƙaunar abin da yake daidai,Kana ƙin abin da yake mugu.Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.

8 Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.

9 Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna.A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye.Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.

10 Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki,Ki manta da mutanenki da danginki.

11 Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki,Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.

12 Mutanen Taya za su kawo miki kyautai,Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.

13 Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun,Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,

14 Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado.Ga 'yan matanta a biye,Aka kawo su wurin sarki.

15 Da farin ciki da murna suka zo,Suka shiga fādar sarki.

16 Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa,Waɗanda za su maye matsayin kakanninka,Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.

17 Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada,Dukan jama'a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.