1 Waƙata ta aminci ce da gaskiya.Ina raira maka ita, ya Ubangiji.
2 Abin da nake yi ba zai zama laifi ba,Yaushe za ka zo wurina?Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.
3 Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan.Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah,Ba ruwana da su.
4 Ba zan yi rashin aminci ba,Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
5 Zan hallakar da mai raɗar abokinsa,Ba zan jure da mutum mai girmankai,Ko mai alfarma ba.
6 Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah,Zan yardar musu si yi zamansu a fādata,Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminciSu yi mini hidima.
7 Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba,Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.
8 A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu,Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.