1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Ka taimake ni yanzu!Ka saurare ni sa'ad da na kira gare ka.
2 Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa,Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.
3 Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina,Ka sa mai tsaro a leɓunana.
4 Ka tsare ni daga son yin mugunta,Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu,Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!
5 Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri,Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai,Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.
6 Mutane za su yarda, cewa maganata gaskiya ce,Sa'ad da aka jefo da masu mulkinsu ƙasa, daga ƙwanƙolin dutse,
7 Kamar itacen da aka faskare, aka daddatse,Haka aka watsar da ƙasusuwansu a gefen kabari.
8 Amma ni, ya Ubangiji Allah, da nake dogara a gare ka,Ina neman kiyayewarka,Kada ka bar ni in halaka!
9 Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini,Daga ashiftar masu aikata mugunta.
10 Ka sa mugaye su fāɗa cikin tarkunansu,Ni kuwa in zo in wuce lafiya.