1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
2 Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!
3 Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
4 Ku shiga Haikalinsa da godiya,Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!Ku gode masa, ku yabe shi!
5 Ubangiji nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce,Amincinsa kuwa har abada abadin ne.