1 Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,Da me zai faru?Ba da amsa, ya Isra'ila!
2 “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,
3 Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,Saboda zafin fushi da suke yi da mu,
4 Da rigyawa ta kwashe mu,Da ruwa yi ci mu,
5 Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”
6 Sai mu gode wa Ubangiji,Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.
7 Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta,Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!
8 Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa,Shi wanda ya yi sama da duniya.