1 Ubangiji Sarki ne,Mutane suna rawar jiki,Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,Duniya ta girgiza.
2 Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.
3 Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,Mai Tsarki ne shi!
4 Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,Ka kawo adalci cikin Isra'ila,Ka kawo adalci da gaskiya.
5 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!Mai Tsarki ne shi!
6 Musa da Haruna firistocinsa ne,Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne.Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.
7 Ya yi magana da su daga girgije,Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.
8 Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka,Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara,Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.
9 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki!Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!