1 Ya Allah, ka kuɓutar da ni,Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka,Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!
2 Ya Allah, kai ne kake kāre ni,Me ya sa ka yashe ni?Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?
3 Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka,Bari su bishe ni,Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka,Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!
4 Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah,Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki,In raira waƙar yabo a gare ka da garayata,Ya Allah, Allahna!
5 Me ya sa nake baƙin ciki?Me ya sa nake damuwa?Zan dogara ga Allah,Zan ƙara yabonsa,Mai Cetona, Allahna.