1 Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji,Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.
2 Na durƙusa a gaban tsattsarkan HaikalinkaIna yabon sunanka.Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka,Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.
3 Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka,Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.
4 Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji,Gama sun riga sun ji alkawaranka.
5 Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi,Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.
6 Ko da yake Ubangiji yana can Sama,Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici.Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.
7 Ko lokacin da nake tsakiyar wahala,Za ka kiyaye ni lafiya,Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata,Za ka kuwa cece ni da ikonka.
8 Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini,Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada.Ka cikasa aikin da ka fara.