1 Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!”Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.
2 Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane,Yă ga ko da akwai masu hikimaWaɗanda suke yi masa sujada.
3 Amma dukansu sun koma baya,Su duka mugaye ne,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,Babu ko ɗaya.
4 Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba?Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne?Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke zaman gari,Ba su yin addu'a gare ni.”
5 Amma za su razana,Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.
6 Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya,Saboda yana dogara ga Ubangiji.
7 Ina addu'a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona!Sa'ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama'arsa,Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki,Jama'ar Isra'ila za su yi murna.