1 Ubangiji makiyayina ne,Ba zan rasa kome ba.
2 Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.
3 Yana ba ni sabon ƙarfi.Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.
4 Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,Gama kana tare da ni!Sandanka na makiyayi da kerenkaSuna kiyaye lafiyata.
5 Ka shirya mini liyafaInda maƙiyana duk za su iya ganina,Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,Ka cika tanduna fal da mai.
6 Hakika, alherinka da ƙaunarkaZa su kasance tare da ni muddin raina.Haikalinka zai zama gidana har abada.