1 Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina,“Zauna nan a damana,Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2 Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce,“Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3 A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka,Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.Kamar yadda raɓa take da sassafe,Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4 Ubangiji ya yi muhimmin alkawari,Ba kuwa zai fasa ba!“Za ka zama firist har abadaBisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
5 Ubangiji yana damanka,Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6 Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma,Ya rufe fagen fama da gawawwaki,Zai kori sarakunan duk duniya.
7 Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya,Ya wartsake ya sami ƙarfi.Zai yi tsayawar nasara.