Zab 17 HAU

Addu'ar Neman Tsari daga Azzalumai

1 Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum,Ka lura da kukana na neman taimako!Ka kasa kunne ga addu'ata,Gama ni ba mayaudari ba ne.

2 Za ka shara'anta shari'ar da za ta gamshe ni,Saboda ka san abin da yake daidai.

3 Ka san zuciyata,Kakan zo gare ni da dare,Ka riga ka jarraba ni sarai,Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba.Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.

4 Zancen aikin sauran mutane,Na yi biyayya ga umarninkaBan bi hanyar rashin hankali ba.

5 Ina tafiya a kan tafarkinka kullum,Ban kuwa kauce ba.

6 Ina addu'a gare ka, ya Allah,Domin kakan amsa mini,Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.

7 Ka bayyana ƙaunarka mai banmamaki,Ya Mai Ceto,Muddin muna kusa da kai mun tsira daga maƙiyanmu.

8 Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu,Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,

9 Daga hare-hare na mugaye.Maƙiyana cike da ƙiyayya sun kewaye ni.

10 Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,

11 Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya,Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.

12 Kamar zakoki suke nema su yayyage ni kaca-kaca,Kamar sagarun zakoki suna fakona a wurin ɓuyarsu.

13 Ka zo, ya Ubangiji,Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su!Ka cece ni da takobinka daga mugaye,

14 Ka cece ni daga gare su da ikonka,Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan,Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu,Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su,Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!

15 Zan gan ka domin ni adali ne,Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.