1 Ya Allah, ka ji kukana,Ka ji addu'ata!
2 Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai,Zan yi kira gare ka!Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.
3 Kai ne kāriyata mai ƙarfiDa take kiyaye ni daga maƙiyana.
4 Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina,Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.
5 Ya Allah, kā ji alkawaraina,Kā kuwa ba ni abin da ya dace,Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.
6 Ka ƙara wa sarki tsawon rai,Ka sa ya rayu dukan lokaci!
7 Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah,Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka.
8 Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin,A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.