1 Ka cece ni, ya Allah!Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
2 Ka sa masu so su kashe ni,A ci nasara a kansu, su ruɗe!Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!
3 Ka sa waɗanda suke mini ba'aSu razana sabili da fāɗuwarsu!
4 Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare kaSu yi murna, su yi farin ciki!Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonkaKullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
5 Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.Kai ne mataimakina da Mai Cetona,Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!