1 A cikin fid da zuciyata,Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.
2 Ka ji kukana, ya Ubangiji,Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!
3 Idan kana yin lissafin zunubanmu,Wa zai kuɓuta daga hukunci?
4 Amma kakan gafarta mana,Domin mu zama masu tsoronka.
5 Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji,Ga maganarsa na dogara.
6 Ina jiran Ubangiji,Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir,I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.
7 Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji,Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce,A koyaushe yana da nufin yin gafara.
8 Zai fanshi jama'arsa Isra'ilaDaga dukan zunubansu.