1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma,Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!
2 Yana kama da man zaitun mai daraja,Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa,Har zuwa wuyan riganunsa.
3 Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon,Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona.A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa,Rai na har abada.