1 Na duba wajen duwatsu,Daga ina taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,Wanda ya yi sama da ƙasa.
3 Ba zai bar ka ka fāɗi ba,Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
4 Makiyayin Isra'ila,Ba ya gyangyaɗi ko barci!
5 Ubangiji zai lura da kai,Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.
6 Ba za ka sha rana ba,Ko farin wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari,Zai sa ka zauna lafiya.
8 Zai kiyaye shigarka da fitarka,Tun daga yanzu har abada.