1 Ubangiji sarki ne!Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne.Hakika duniya ta kahu sosai a inda take,Ba kuwa za ta jijjigu ba.
2 Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko,Kana nan tun fil azal.
3 Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu,Suna ta da muryarsu da ruri.
4 Ubangiji yana mulki cikin Sama,Mulkinsa mafifici ne,Fiye da rurin teku,Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.
5 Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji,Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai,Har abada abadin.