1 Ka cece ni, ya Ubangiji,Ba sauran mutanen kirki,Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.
2 Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya,Suna ruɗin junansu da yaudara.
3 Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru,Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!
4 Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama,Ba kuwa wanda zai hana mu.Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?”
5 Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu,Domin ana zaluntar masu bukata,Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi.Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”
6 Alkawaran Ubangiji abin dogara ne,Alkawarai ne na ainihi kamar azurfaDa aka tace har sau bakwai cikin matoya.
7 Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji,Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane.
8 Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga,Suna ta yabon abin da yake mugunta.