Zab 19 HAU

Ayyukan Allah da Shari'arsa

1 Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!

2 Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.

3 Ba magana ko kalma da aka hurta,Ba wani amon da aka ji,

4 Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya.Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,

5 Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.

6 Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan.Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.

7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,Tana wartsakar da rai.Umarnan Ubangiji abin dogara ne,Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.

8 Ka'idodin Ubangiji daidai suke,Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi.Umarnan Ubangiji daidai suke,Sukan ba da fahimi ga zuciya.

9 Daidai ne a bauta wa Ubangiji,A ci gaba da yi har abada.Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne,A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.

10 Abin da ake so ne fiye da zinariya,I, fiye da tatacciyar zinariya ma,Sun fi zuma zaƙi,I, fiye da tatacciyar zuma ma.

11 Suna ba ni ilimi, ni baranka,Ina samun ladan yin biyayya da su.

12 Ba mai iya ganin kuskuren kansa,Ka cece ni daga ɓoyayyun laifofi!

13 Ka tsare ni kuma daga laifofi na fili,Kada ka bari su mallake ni.Sa'an nan zan zama kamili,In kuɓuta daga mugun zunubi.

14 Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka,Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!