1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji,Suna kama da Dutsen Sihiyona,Wanda ba zai jijjigu ba, faufau.Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.
2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima,Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa,Daga yanzu har abada.
3 Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba,Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.
4 Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri,Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!
5 Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu,Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta!Salama ta kasance tare da Isra'ila!