1 Ka amsa mini sa'ad da na yi kira,Ya Allah, madogarata!Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona.Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!
2 Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina?Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza,Da bin abin da yake na ƙarya?
3 Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa,Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.
4 Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku,Ku yi tunani da gaske a kan wannanA kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.
5 Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace,Ku kuma dogara gare shi.
6 Akwai mutane da yawa da suke cewa,“Da ma a sa mana albarka!”Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!
7 Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne,Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.
8 Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni,Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.