1 Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini!Kada ka hukunta ni da fushinka!
2 Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis,Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.
3 Duk na damu ƙwarai da gaske.Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji?
4 Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni,Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.
5 Ba za a tuna da kai a lahira ba,Ba wanda zai yabe ka a can!
6 Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki,Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana.Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.
7 Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka,Har da ƙyar nake iya gani,Duk kuwa saboda abokan gābana!
8 Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta!Ubangiji yana jin kukana.
9 Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako,Yana kuwa amsa addu'o'ina.
10 Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu,Suna cikin matsanancin ruɗami,Za a kwashe su farat ɗaya.