1 Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji,Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!
2 Suna magana a kaina, suna cewa,“Allah ba zai taimake shi ba!”
3 Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari,Kana ba ni nasara,Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
4 Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako,Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.
5 Na kwanta na yi barci,Na kuwa tashi lafiya lau,Gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6 Ba na jin tsoron dubban abokan gābaWaɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.
7 Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,Ka hallakar da dukan mugaye.
8 Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,Bari yă sa wa jama'arsa albarka!