1 Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntarDa maƙiyanka suka tsananta maka da ita,Tun kana ƙarami!
2 “Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,Tun ina ƙarami,Amma ba su yi nasara da ni ba.
3 Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.
4 Amma Ubangiji mai adalci,Ya 'yantar da ni daga bauta.”
5 Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,A yi nasara da su a kuma kore su!
6 Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.
7 Ba wanda zai tattara ta,Ya ɗaure ta dami dami.
8 Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce,“Ubangiji ya sa maka albarka!” ba,Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!”