1 Sa'ad da nake shan wahala,Na yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa amsa mini.
2 Ka cece ni, ya Ubangiji,Daga maƙaryata da masu ruɗi!
3 Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku?Yaya zai hukunta ku?
4 Da kibau masu tsini na mayaƙa,Da garwashin wuta zai hukunta ku!
5 Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,Ko tare da mutanen Kedar!
6 Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!
7 Sa'ad da nake maganar salama,Su sai su yi ta yaƙi.