Zab 33 HAU

Waƙar Yabo

1 Dukanku adalai ku yi murna,A kan abin da Ubangiji ya yi,Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya!

2 Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya.Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.

3 Ku raira masa sabuwar waƙa,Ku kaɗa garaya da gwaninta,Ku kuma raira waƙa da ƙarfi!

4 Kalmomin Ubangiji gaskiya ne,Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne.

5 Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya,Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya.

6 Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa,Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.

7 Ya tattara tekuna wuri ɗaya.Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya.

8 Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji!Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya!

9 Da magana ya halicci duniya,Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.

10 Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma,Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.

11 Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada.Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada.

12 Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta,Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!

13 Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan 'yan adam.

14 Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.

15 Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.

16 Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba,Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.

17 Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara,Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.

18 Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa,Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.

19 Yakan cece su daga mutuwa,Yakan rayar da su a lokacin yunwa.

20 Ga Ubangiji muke sa zuciya,Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.

21 Saboda da shi muke murna,Muna dogara ga sunansa mai tsarki.

22 Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji,Da yake a gare ka muke sa zuciya.