Zab 34 HAU

Yabo domin Kuɓuta

1 Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin,Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.

2 Zan yabe shi saboda abin da ya yi,Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna!

3 Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni,Mu yabi sunansa tare!

4 Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini,Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.

5 Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,Ba za su ƙara ɓacin rai ba.

6 Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa.Ya cece su daga dukan wahalarsu.

7 Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji,Ya cece su daga hatsari.

8 Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri!Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!

9 Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka,Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.

10 Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa,Amma masu biyayya ga Ubangiji,Ba abu mai kyau da sukan rasa.

11 Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni,Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.

12 Kuna so ku ji daɗin rai?Kuna son tsawon rai da farin ciki?

13 To, ku yi nisa da mugun baki,Da faɗar ƙarairayi.

14 Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri,Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.

15 Ubangiji yana lura da adalai,Yana kasa kunne ga koke-kokensu,

16 Amma yana ƙin masu aikata mugunta,Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.

17 Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne,Yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai,Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.

19 Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa,Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.

20 Ubangiji yakan kiyaye shi sosai,Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.

21 Mugunta za ta kashe mugu,Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.

22 Ubangiji zai fanshi bayinsa,Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafakaZa a bar su da rai.