Zab 40 HAU

Wakar Yabo

1 Na yi ta jiran taimakon Ubangiji,Sa'an nan ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana.

2 Ya fisshe ni daga rami mai hatsari!Ya aza ni a kan dutse lafiya lau.Ya kawar mini da tsoro.

3 Ya koya mini raira sabuwar waƙa,Waƙar yabon Allahnmu.Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata,Za su kuwa dogara ga Ubangiji.

4 Mai farin ciki ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,Wanda bai juya ga gumaka ba,Ko ya haɗa kai da masu sujada ga allolin karya.

5 Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna.Ba wani kamarka!Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka,Sun fi ƙarfin in faɗa.

6 Ba ka bukatar baye-baye da hadayu,Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawaNa dabbobi a bisa bagade ba,Ko baya-baye don a kawar da zunubai.A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.

7 Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare niSuna a Littafin Shari'a.

8 Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah!Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”

9 A taron dukan jama'arka, ya Ubangiji,Na ba da albishir na cetonka.Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.

10 Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba,Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe.Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka,Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.

11 Ya Ubangiji, na sani ba za ka fasa yi mini jinƙai ba!Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.

12 Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa!Alhakin zunubaina ya tarar da ni,Har ba na iya gani,Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.

13 Ka cece ni, ya Allah,Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!

14 Ka sa masu so su kashe ni,A ci nasara a kansu, su ruɗe!Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalainaSu koma baya, su sha kunya!

15 Ka sa waɗanda suke mini ba'aSu razana sabili da faɗuwarsu!

16 Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare kaSu yi murna, su yi farin ciki!Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonkaKullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”

17 Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.Kai ne mataimakina da Mai Cetona,Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!