1 Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa?Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?
2 Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta,Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.
3 Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa,Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.
4 Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!”Wannan ne abin da mugu yake tunani.
5 Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.Ba zai fahimci hukuncin Allah ba,Yana yi wa abokan gābansa duban raini.