6 Yana ce wa kansa “Ba zan taɓa fāɗuwa ba,Ba zan taɓa shan wahala ba.”
7 Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana,Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.
8 Yakan ɓuya cikin ƙauyuka,Yă jira a can har yă kashe marasa laifi.Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,
9 Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki.Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama,Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!
10 Yakan ragargaza kāsasshe,Yă gwada masa ƙarfi, yă ci nasara a kansa.
11 Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba!Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”
12 Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni!Kada ka manta da waɗanda ake zaluntarsu, ya Allah!