1 Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!
2 Kada ka ɓoye mini sa'ad da nake shan wahala!Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa'ad da na yi kira!
3 Raina ya ɓace kamar hayaƙi,Jikina yana ƙuna kamar wuta.
4 An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa,Ba ni da marmarin cin abinci.
5 Ina nishi da ƙarfi,Ba abin da ya ragu gare ni,In banda ƙashi da fata.
6 Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada,Kamar mujiya a kufai.