10 Sabili da fushinka da hasalarka.Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.
11 Raina kamar inuwar maraice yake,Kamar busasshiyar ciyawa nake.
12 Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada,Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.
13 Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona,Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai,Wannan shi ne lokacin!
14 Bayinka suna ƙaunarta,Ko da yake an hallakar da ita,Suna jin tausayinta,Ko da yake ta zama kufai.
15 Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji,Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.
16 Sa'ad da Ubangiji ya sāke gina SihiyonaZai bayyana girmansa.