4 An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa,Ba ni da marmarin cin abinci.
5 Ina nishi da ƙarfi,Ba abin da ya ragu gare ni,In banda ƙashi da fata.
6 Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada,Kamar mujiya a kufai.
7 Kwana nake ba barci,Na zama kamar tsuntsun da yake fama da kewaA bisa kan ɗaki.
8 Maƙiyana suna cin mutuncina dukan yini.Waɗanda suke mini ba'a,Suna la'antarwa da sunana.
9 Toka ce abincina,Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,
10 Sabili da fushinka da hasalarka.Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.