1 Ka yabi Ubangiji, ya raina!Ka yabi sunansa mai tsarki!
2 Ka yabi Ubangiji, ya raina,Kada ka manta da yawan alherinsa.
3 Ya gafarta dukan zunubaina,Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.
4 Ya cece ni daga kabari,Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.
5 Ya cika raina da kyawawan abubuwa,Don in zauna gagau,Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.
6 Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari'a ta gaskiya.Yakan ba su hakkinsu.