19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama,Shi yake sarautar duka.
20 Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku,Ku da kuke biyayya da umarnansa,Kuna kasa kunne ga maganarsa!
21 Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a Sama,Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!
22 Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa,A duk inda yake mulki!Ka yabi Ubangiji, ya raina!