3 Ya gafarta dukan zunubaina,Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.
4 Ya cece ni daga kabari,Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.
5 Ya cika raina da kyawawan abubuwa,Don in zauna gagau,Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.
6 Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari'a ta gaskiya.Yakan ba su hakkinsu.
7 Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa.Ya yardar wa jama'ar Isra'ila su ga manyan ayyukansa.
8 Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma,Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.
9 Ba zai yi ta tsautawa kullum ba,Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.