7 Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa.Ya yardar wa jama'ar Isra'ila su ga manyan ayyukansa.
8 Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma,Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.
9 Ba zai yi ta tsautawa kullum ba,Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.
10 Yakan yi mana rangwame sa'ad da yake hukunta mu,Ko sa'ad da yake sāka mana saboda zunubanmu da laifofinmu.
11 Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya,Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.
12 Kamar yadda gabas take nesa da yamma,Haka nan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.
13 Kamar yadda uba yake yi wa 'ya'yansa alheri,Haka nan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.