17 A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu,A bisa itatuwan fir shamuwa suke yin sheƙa.
18 A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama,Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.
19 Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.
20 Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.
21 Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta,Suna neman abincin da Allah zai ba su.
22 Sa'ad da rana ta fito,Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.
23 Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,Su yi ta aiki har maraice ya yi.