4 Iska ce jakadanka,Walƙiya kuwa ita ce baiwarka.
5 Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta,Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.
6 Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba,Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
7 Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa,Sai ya tsere,Sa'ad da ya ji ka daka tsawa,Sai ya sheƙa a guje.
8 Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka,Wurin da ka shirya masa.
9 Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba,Don kada ya sāke rufe duniya.
10 Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka,Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.