24 Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa,Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.
25 Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,Suka yi wa bayinsa munafunci.
26 Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.
27 Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.
28 Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29 Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.
30 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.