26 Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.
27 Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.
28 Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29 Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.
30 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.
31 Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.
32 Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.