28 Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29 Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.
30 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.
31 Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.
32 Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.
33 Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,Ya kakkarya itatuwansu.
34 Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.